Kenya : Kotun Koli Ta Yi Na'am Da Sake Zaben Kenyatta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25581-kenya_kotun_koli_ta_yi_na'am_da_sake_zaben_kenyatta
Kotun koli a kasar Kenya ta amince da sake zaben shugaba Uhuru Kenyatta a wani wa'adin shugabanci na shekaru biyar masu zuwa.
(last modified 2018-08-22T11:31:01+00:00 )
Nov 20, 2017 10:03 UTC
  • Kenya : Kotun Koli Ta Yi Na'am Da Sake Zaben Kenyatta

Kotun koli a kasar Kenya ta amince da sake zaben shugaba Uhuru Kenyatta a wani wa'adin shugabanci na shekaru biyar masu zuwa.

Kotun ta kuma yi watsi da korafe-korafe guda biyu da aka gabatar  mata na neman soke zaben na ranar 26 ga watan Oktoba da ya gabata.

Shugaban kotun, David Maraga, ya ce korafe korafen da aka gabatar basu da tushe.

Sake zaben Uhuru Kenyatta a zaben na ranar 26 ga watan Oktoba bai zo da mamaki ba, kasancewar 'yan adawa sun kaurace masa.