Harin Ta'addanci Ya Hallaka Mutane Biyu A Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25587-harin_ta'addanci_ya_hallaka_mutane_biyu_a_kamaru
Harin kunar bakin wake ya hallaka fararen hula a arewacin kasar kamaru
(last modified 2018-08-22T11:31:01+00:00 )
Nov 20, 2017 19:07 UTC
  • Harin Ta'addanci Ya Hallaka Mutane Biyu A Kamaru

Harin kunar bakin wake ya hallaka fararen hula a arewacin kasar kamaru

Kamfanin dillancin labaran kasar faransa ya nakalto wata majiya ta kusa da dakarun tsaron kasar Kamaru na cewa wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a kasuwar Kolofata mai yawan cinkoson jama'a dake arewacin kasar mai iyaka da tarayyar Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutuwar mutane biyu tare da jikkatar wasu 20 na daban.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, to saidai ana zargin kungiyar ta'addancin nan ta boko haram wacce ta saba kai hare-haren ta'addanci a yankin da kai harin.

Kasar kamaru dai ta fara yakar kungiyar boko haram a shekarar 2014, hare-haren kungiyar boko haram ya hallaka mutane sama da jami'an tsaro da fararen dubu biyu a arewacin kasar kamaru.