D-Congo Ta Kira Yi Jakadanta Daga Libya Akan Cinikin Bayi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25667-d_congo_ta_kira_yi_jakadanta_daga_libya_akan_cinikin_bayi
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato ministan harkokin wajen kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Leonardo Sheet OKITUNDU, yana kiran 'yan kasarsa da ke Libya da su koma gida.
(last modified 2018-08-22T11:31:02+00:00 )
Nov 23, 2017 06:38 UTC
  • D-Congo Ta Kira Yi Jakadanta Daga Libya Akan Cinikin Bayi

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato ministan harkokin wajen kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Leonardo Sheet OKITUNDU, yana kiran 'yan kasarsa da ke Libya da su koma gida.

Ministan harkokin wajen kasar ta Demokradiyyar Congo Leonardo Sheet OKITUNDU ya kuma bukaci ganin an shigar da batun 'yan gudun hijira a cikin ajandar aiki ta tattuanwar a taro tsakanin Afirka da turai da za a yi a birnin Abidjan na kasar Cote De Voire.

Ita ma kasar Burkina Faso ta kira yi jakadanta daga kasar ta Libya domin nuna kin amincewa da sayar da bakaken fata a matsayin bayi a wannan kasa.

Jim kadan bayan yaduwar labarin cinikin 'yan Afirka a matsayin bayi a kasar Libya, kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suka fara maida martani da yin Allah wadai.