Aljeriya Ta Soki Cinikayyar Bakin Haure 'Yan Kasashen Afirka
Shugaban cibiyar kare hakin bil-adama na kasar Aljeriya ya soki cinikayyar bakin haure a kasar Libiya.
Jaridar Al-arab ta nakalto Papa Sayyid Lakhdar bn Zuruki shugaban cibiyar kare hakin bil-adama na kasar Aljeriya a gefen taron yaki da cin zarafin mata na kasashen Afirka na cewa ya zama wajibi abi dokar kare hakokin bil'adama yayin da ake mayar da bakin haure zuwa kasashen su, sannan ya tabbatar da cewa wajibi ne a mutunta dokokin 'yan gudun hijra mata musaman ma wadanda suke dauke da juna biyu.
Abin da dokar kare hakin bil-adama ta duniya ta bayyana duk 'yar gudin hijrar dake da juna biyu ba za a mayar da ita kasar ta ba har sai ta haife abin da take dauke da shi.
A makon da ya gabata, cibiyar kare hakin bil-adama ta kasar Algeriya ta sanar da cewa gwamnatin kasar ba ta yi abin da ya dace ba a game da bakin haure, wannan sanarwa na zuwa ne bayan da hukumar kare hakin bil-adama ta MDD ta zargi gwamnati ta Aljeriya da kame bakin haure tare da fitar da su daga cikin kasar su.