An Cimma Yarjejniyar Dauke Bakin Haure Daga Libya
Shugabannin tarayyar Afirka a kuma na turai da MDD sun cimma yarjejniyar fitar da bakin hauren cikin gaggawa daga Libya
Shugaban kasar Faransa Emanuel Macron da yake halartar taron da ake yi a birnin Abidjan na kasar Cote De Voire, ya ce shugaban rikon kwaryar kasar Libya Fa'iz Siraj ya bada tabbacin nan da wasu kwanaki za a sami damar kai wa ga wuraren da 'yan gudun hijirar suke.
Babban jami'i a kwamitin sulhu da tsaro na tarayyar Afirka, Isma'il Sharki ya jaddada cewa; Abinda kungiyoyin yankin da na duniya suka cimmawa shi ne samar da yanayi na gaggawa domin 'yantar da bakin hauren da kuma fitar da su daga cikin kasar.
A cikin kwanakin nan ne rahotannin suke nuni da yadda ake sayar da yan gudun hijira daga Afirka a matsayin bayi.