Bukatar Fira Ministan Libiya Ta Neman Dagewa Kasarsa Takunkumin Sayan Makamai
Fira ministan gwamnatin hadin kan kasar Libiya ya bukaci dage wa kasarsa takunkumin sayan makamai da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa kasar ta Libiya tun a shekara ta 2011.
A ganawarsa da sakataren tsaron kasar Amurka Jim Mattis a birnin Washington: Fira ministan Libiya Fayyaz Assarraj ya bayyana cewa: Libiya tana fuskantar kalubale masu yawa musamman matsalar kungiyoyin 'yan ta'adda, sakamakon haka tana jaddada fatan ganin gwamnatin Amurka ta taimaka mata wajen ganin an dage mata takunkumin hana sayan makamai da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba mata, kuma koda dage takunkumin zai kasance mataki - mataki ne ta hanyar fara dage takunkumin kan dakarun kare fadar shugaban kasa, sannan dakarun tsaron gabar tekun kasar ta Libiya.
Tun bayan bullar rikici da tashe-tashen hankula a kasar Libiya a shekara ta 2011, kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kakaba takunkumin hana sayar wa kasar ta Libiya makamai ta hanyar fitar da kuduri mai lamba 1970, inda nassin kudurin ya hana duk wata kasa da take matsayin mamba a Majalisar Dinkin Duniya sayarwa Libiya makamai.
A fili yake cewa: Gwamnatin hadin kan kasar Libiya tana da masaniyar cewa: Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya dauki matakin kakaba takunkumin hana sayar da makamai kan kasar ta Libiya ce a shekara ta 2011 da nufin karya karfin sojojin gwamnatin Libiya karkashin shugabancin marigayi Mu'ammar Gaddafi domin 'yan tawayen kasar su samu damar kawo karshen mulkin Gaddafi a kasar, inda a bayan kifar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi, makaman kasar suka koma hannun kungiyoyin 'yan tawayen Libiya da mafi yawansu suka rikide zuwa kungiyoyin 'yan ta'adda masu tsaurin ra'ayin addinin Islama, don haka a halin yanzu gwamnatin Libiya tana bukatar makamai da nufin kalubalantar kungiyoyin.
A gefe guda kuma a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya take ci gaba da jaddada batun aiwatar da kudurin hana sayar da makamai kan kasar Libiya, amma ta bayan fage manyan kasashen duniya suna ci gaba da fataucin makaman zuwa kasar ta Libiya, inda a halin yanzu kasar ta zame tamkar cibiyar fataucin makamai a nahiyar Afrika, kuma abin bakin ciki, makaman suna shiga hannun kungiyoyin 'yan ta'adda ne da suke aiwatar da hare-haren wuce gona da iri kan al'ummun kasashen nahiyar Afrika da ma yankin gabas ta tsakiya.
Sakamakon haka a bangare guda Majalisar Dinkin Duniya tana da'awar kare kudurin kwamitin tsaron Majalisar mai lamba 1970 kan kasar Libiya, yayin da a daya bangaren manyan kasashen duniya suke ci gaba da fataucin makamai zuwa kasar domin azurta kai lamarin da ke ci gaba da janyo bullar tashe-tashen hankula a ciki da wajen kasar ta Libiya, don haka batun shawo kan matsalolin siyasa da na tsaro a kasar ta Libiya suka ci tura.