Libya: An Kashe Sojoji Biyu A Fada Da 'Yan ta'adda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26009-libya_an_kashe_sojoji_biyu_a_fada_da_'yan_ta'adda
Kakakin sojojin gwamnatin Libya ne ya sanar da kashe sojojin kasar a fada da 'yan ta'adda a yankin Banighazi.
(last modified 2018-08-22T11:31:05+00:00 )
Dec 04, 2017 18:48 UTC
  • Libya: An Kashe Sojoji Biyu A Fada Da 'Yan ta'adda

Kakakin sojojin gwamnatin Libya ne ya sanar da kashe sojojin kasar a fada da 'yan ta'adda a yankin Banighazi.

Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya kuma ambato kakanin sojan na Libya  Milud al-zawy, yana ci gaba da cewa; Sojojin suna ci gaba da fada da yan ta'addar da su ke a gabacin kasar.

 Banighazi da ke gabacin Libya yana a matsayin yankin da 'yan ta'adda su ka yi dandazo, tun bayan faduwar gwamnatin Khaddafi a 2011.

 Janar Halifa Hatfar wanda yake samun goyon bayan wasu kasashen larabawa ya bude yaki akan kungiyoyin 'yan ta'adda shekaru uku kenan a jere.