An yankewa Mayakan boko haram 89 hukuncin kisa a Kamaru
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2602-an_yankewa_mayakan_boko_haram_89_hukuncin_kisa_a_kamaru
Majiyar Shara'a ta kasar Kamaru ta ce Kotun Soja a Arewacin kasar ta yanke hukuncin kisa ga mayakan boko haram 89
(last modified 2018-08-22T06:58:00+00:00 )
Mar 18, 2016 01:30 UTC
  • An yankewa Mayakan boko haram 89 hukuncin kisa a Kamaru

Majiyar Shara'a ta kasar Kamaru ta ce Kotun Soja a Arewacin kasar ta yanke hukuncin kisa ga mayakan boko haram 89

A jiya Alkhamis wani jami'in shara'a na kasar Kamaru da ya bukaci a boye sunansa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai France Press cewa a ranar Larabar da ta gabata kotun sojin arewacin kasar ta yanke hukuncin kisa kan mayakan boko haram 89, kuma wannan hukunci da aka yanke na karshe ne babu batun daukaka kara.

Har ila yau jami'in ya kara da cewa a kwai mutanesama da dubu guda da suke tsare , kan zarkinsu da alaka tare da boko haram da s kuma uke jiran shara'a a gidajen kurkukun kasar.

A watan Augustan shekarar da ta gabata, Kotun kasar Tchadi ta yankewa mayakan boko haram 10 hukumcin kisa bayan da ta kama su da laifin kai harin tagwayen bama-bamai a Injamena babbar birnin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 28.

Ministan Sadarwar Kamaru ya sanar da cewa daga farkon wannan shekara da muke cikin mayakan boko haram din sun kaddamar da hare-haren bamai bamai sama da 15 a kasar, kuma daga shekarar 2013 zuwa yanzu sun kashe fararen da jami'an tsaro sama da dubu daya a yankin arewacin kasar.