An Gudanar Da Zanga-Zangar Bukatar Kawo Karshen Bautar Da Mutane
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26205-an_gudanar_da_zanga_zangar_bukatar_kawo_karshen_bautar_da_mutane
Masu adawa da bautar da mutane sun gudanar da zanga-zangar lumana a gaban ofishin jakadancin Libya da ke birnin London na kasar Britania, inda suka bukaci gwamnatin Britania ta takurawa kasar Libya saboda wannan dabi'ar ta bautar da mutane.
(last modified 2018-08-22T11:31:07+00:00 )
Dec 10, 2017 11:55 UTC
  • An Gudanar Da Zanga-Zangar Bukatar Kawo Karshen Bautar Da Mutane

Masu adawa da bautar da mutane sun gudanar da zanga-zangar lumana a gaban ofishin jakadancin Libya da ke birnin London na kasar Britania, inda suka bukaci gwamnatin Britania ta takurawa kasar Libya saboda wannan dabi'ar ta bautar da mutane.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ce an gudanar da zanga -zangar ne a jiya Asbar a gaban ofishin jakadancin kasar Libya a London bayan an watsa wani faifan bidiyo wanda tashar talabijin ta CNN ta yi, inda aka nuna yadda aka saida wani matashi a wata kasuwar baya a birnin Tripoli babban birnin kasar ta Libya. 

A ranar 7 ga watan Disamba da muke ciki ne kwamitin tsaro na MDD ya yi Allah wadai da saida bayi a kasar Libya, ya kuma dauke shi a matsayin sabawa hakkin bil'adama ne. 

Kofi De Lume daya daga cikin masu zanga-zangar ya fadawa Associated Press kan cewa cinikin bayi a Libya ba sabon abu ba ne, sai dai dole ne kasashen duniya su kawo karshen hijirar da yan aArika suke yi zuwa turai.