Kamaru : An Kashe Jami'an Tsaro Hudu A Kudu Maso Yamma
(last modified Tue, 19 Dec 2017 11:04:53 GMT )
Dec 19, 2017 11:04 UTC
  • Kamaru : An Kashe Jami'an Tsaro Hudu A Kudu Maso Yamma

Rahotanni daga Kamaru na cewa jami'an tsaron kasar na Jandarma hudu ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai masu a yankin masu magana da harshen turancin Ingilishi a Kudu maso yammacin kasar.

Wani jami'in hukumar tsaro a kasar Kamaru ya bayyana cewa, an kai harin ne a wani sansanin soja dake kudu maso yammacin kasar da ke dab da iyakar kasar da Nijeriya.

Koda yake dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma tuni aka fara zargin 'yan aware dake yankin da kai harin.

Wannan dai ya sanya adadin jami'an tsaro da aka kashe a wannan yankin a kasa da wata biyar ya haura zuwa 15.