MDD Tana Kokarin Hada Kan Yan Siyasa A Kasar Libya
(last modified Wed, 20 Dec 2017 06:23:28 GMT )
Dec 20, 2017 06:23 UTC
  • MDD Tana Kokarin Hada Kan Yan Siyasa A Kasar Libya

A kokarin da MDD take yi don hada kan yan siyasar kasar Libya manzon musamman na Majalisar a kasar ya ziyarci majalisar dokokin kasar da ke zama a garin Tabruk daga gabacin kasar a jiya Talata.

kamfanin dillancin labaran Spotnik na Rasha ya nakalto Gassan Salama jakadan MDD na musamman a kasar Libya yana cewa haduwarsa da yan majalisar dokokin kasar ta Libya a Tabruk yana da muhimmanci don sun tattauna batun hadin kan kasa da kuma aiki tare don fitar da kasar daga mummunan halin da take ciki. 

Salama ya gana da yan majalisar dokokin kasar ta Libya a Tabruk ne kwanaki biyu kacal da wata sanarwar da Janar Halifa Haftar mai ritaya kuma wanda yake da karbuwa a majalisar yake cewa, yarjejeniyar Shukhairat tsakanin shuwagabannin yan siyasar kasar ta Libya ta gama aiki, kuma ba ta da wani amfani.

MDD ce ta jagoranci yan siyasar kasar a shekara ta 2015 a garin Sukhairat na kasar Morocco inda shuwagabannin siyasar kasar ta Libya suka amince su kafa gwamnatin hadin kan kasa sannan daga baya a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar.