Afirka Ta Kudu Na Shirin Rage Alakarta Ta Diplomasiyya Da H.K. Isra'ila
Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta Kudu ta sanar da shirin da take da shi na rage alakar kasar Afirka ta Kudun da haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin mayar da martani ga matakin baya-bayan nan da shugaban Amurka ya dauka na sanar da Kudus a matsayin babban birnin HKI.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar Jam'iyyar ta ANC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a yau din nan Alhamis inda ta bukaci gwamnatin Afirka ta Kudun da ta gaggauta rage alakarta ta diplomasiyya da HKI zuwa ga ofishin alaka da sadarwa maimakon ofishin jakadanci.
Shi ma a nasa bangaren sabon sakatare janar na jam'iyyar ta ANC, Ace Magashule, ya ce wakilan jam'iyyar sun dau wannan matsayar ne don nuna goyon bayansu a aikace ga al'ummar Palastinu da ake zalunta, don haka suka bukaci da a mayar da ofishin jakadancin Afirka a 'Isra'ila' zuwa ga karamin ofishi na sadarwa kawai.
Jami'iyyar dai ta dau wannan matsaya ne a karshen taronta na kasa na kwanaki biyar da ta gudanar inda aka zabi mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudun Cyril Ramaphosa a matsayin sabon shugaban jam'iyyar wanda kuma ake ganin zai iya zama shugaban kasar a zaben da za a gudanar a shekara ta 2019 don maye gurbin shugaban kasar na yanzu Jacob Zuma.