Ma'aikatar Shari'ar Libiya Ta Musanta Labarin Batar Sa'adi Gaddafi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26621-ma'aikatar_shari'ar_libiya_ta_musanta_labarin_batar_sa'adi_gaddafi
Shugaban bangaren bincike na Ma'aikatar shari'ar kasar Libiya ya musantar labarin da ke yawo na cewa dan tsohon shugaban kasar Libiya Mu'ammar Gaddafi, wato Sa'adi Gaddafi ya bata, yana mai cewa har ya zuwa yanzu Sa'adi yana nan a tsare a birnin Tripoli.
(last modified 2018-08-22T11:31:11+00:00 )
Dec 23, 2017 05:23 UTC
  • Ma'aikatar Shari'ar Libiya Ta Musanta Labarin Batar Sa'adi Gaddafi

Shugaban bangaren bincike na Ma'aikatar shari'ar kasar Libiya ya musantar labarin da ke yawo na cewa dan tsohon shugaban kasar Libiya Mu'ammar Gaddafi, wato Sa'adi Gaddafi ya bata, yana mai cewa har ya zuwa yanzu Sa'adi yana nan a tsare a birnin Tripoli.

Kamfanin dillancin labaran Iran (IRNA) ya ce Shugaban bangaren bincike na Ma'aikatar shari'ar kasar Libiya, Al-Sadiq al-Sur, ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani  ga labaran da suke yawo na bacewar Sa'adi Gaddafin inda ya ce Sa'adi, dan tsohon shugaba Gaddafi na uku, yana nan a tsare yana fuskantar shari'a bisa zargin da ake masa na hannu cikin dirar mikiyan da aka yi wa masu adawa da tsohuwar gwamnatin Libiya.

A ranar Talatar da ta gabata ce dai iyalan marigayi Gaddafin suka sanar da cewa tsawon lokaci kenan aka katse duk wata hanyar da suke magana da Sa'adi, don haka ba su da wani labari dangane da halin da yake ciki.

A shekara ta 2014 ne dai mahukuntan kasar Nijar suka mika Sa'adi Gaddafi ga mahukutan kasar Libiyan bayan ya shafe shekaru a kasar ta Nijar da ya gudu zuwa can din bayan kifar da gwamnatin mahaifin nasa a shekara ta 2011.