Kungiyar Boko Haram Ta Kai Hari A Arewacin Kamaru.
Wani dan kunar baki wake da ake kyautata zaton dan kungiyar boko haram ne ya kai arewacin kasar kamaru, lamarin da ya yi sanadiyar hallakarsa da kuma mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu da dama na daban.
Kafafen yada labaran kasar Kamaru sun sanar a wannan lahadi cewa, wani dan kunar bakin wake da ake kyautata zaton dan kungiyar boko haram ne ya tarwatsa kansa a wani karamin gari dake arewacin kasar Kamaru, lamarin da ya yi sanadiyar hallakar sa da kuma mutuwar wani farar hula guda tare da jikkata wasu kimanin 30 na daban.
Ya zuwa yanzu babu wani karin bayyani da gwamnati ta yi a game da harin.
Tun a shekarar 2009, kungiyar boko haram ta fara kai hare-hare a arewacin Najeriya, a shekarar 2013 kuma kungiyar ta fadada kai hare-haren ta zuwa kasashen Nijer, Chadi da arewacin Kamaru.kasawar gwamnatin Najeriya da ta gabata ya sanya kungiyar ta boko haram mamaye wasu gariruwa dake arewacin kasar.
Kididdigar majalisar dinkin duniya ta yi nuni da cewa kimanin mutane 20,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin na Boko Haram, yayin da wasu fiye da miliya 2.6 suka yi hijra daga gidajensu, inda a halin yanzu suke tsugunne a sansanonin 'yan gudun hijira, ko kuma suke nemi mafuka a wasu biranan arewacin Najeriya da kuma kasashe makwafta.