Gwamnatin Kamaru Zata Fuskanci Yan Aware Da Gaske A Cikin Sabuwar Shekara
Shugaban kasar Kamaru Mr Paul Biya ya bayyana cewa gwamnatinsa zata fuskanci yan aware a yankin da ake magana da turanci a kudancin kasar da gaske a sabuwar shekaran da ta kama.
Tashar radion kasar faransa ta kasa da kasa ta nakalto shugaba Biya yana fadar haka a jawabinsa na sabuwar shekara a jiya da dare.
Shugaba biyu ya ce a sabuwar shekara ta 2018 duk wanda yake dauke da makami yake kuma kokarin hana zaman lafiya a kasar gwamnatinsa ba zata dauke shi da sauki ba. Ya kuma kara da ce hanyar tattaunawa kadai ita ce hanyar kawo zaman lafiya da fahintar juna a kasar.
Mutanen kasar Kamaru masu magana da harshen turanci su ne kashi 20% na yawan mutanen kasar suna kokawa kan cewa an waresu a rabon mukaman gwamnatin, shiga ayyukan tsaronsa da kuma karatu a tsare-tsarenn gwamnatin kasar na yanzu. Don haka ne a shekaran da ta gabata aka yi ta samun tashe tashen hankula a yankin.