Gwamnatin Kamaru Zata Fuskanci Yan Aware Da Gaske A Cikin Sabuwar Shekara
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26909-gwamnatin_kamaru_zata_fuskanci_yan_aware_da_gaske_a_cikin_sabuwar_shekara
Shugaban kasar Kamaru Mr Paul Biya ya bayyana cewa gwamnatinsa zata fuskanci yan aware a yankin da ake magana da turanci a kudancin kasar da gaske a sabuwar shekaran da ta kama.
(last modified 2018-08-22T07:01:13+00:00 )
Jan 01, 2018 08:16 UTC
  • Gwamnatin Kamaru Zata Fuskanci Yan Aware Da Gaske A Cikin Sabuwar Shekara

Shugaban kasar Kamaru Mr Paul Biya ya bayyana cewa gwamnatinsa zata fuskanci yan aware a yankin da ake magana da turanci a kudancin kasar da gaske a sabuwar shekaran da ta kama.

Tashar radion kasar faransa ta kasa da kasa ta nakalto shugaba Biya yana fadar haka a jawabinsa na sabuwar shekara a jiya da dare.

Shugaba biyu ya ce a sabuwar shekara ta 2018 duk wanda yake dauke da makami yake kuma kokarin hana zaman lafiya a kasar gwamnatinsa ba zata dauke shi da sauki ba. Ya kuma kara da ce hanyar tattaunawa kadai ita ce hanyar kawo zaman lafiya da fahintar juna a kasar. 

Mutanen kasar Kamaru masu magana da harshen turanci su ne kashi 20% na yawan mutanen kasar suna kokawa kan cewa an waresu a rabon mukaman gwamnatin, shiga ayyukan tsaronsa da kuma karatu a tsare-tsarenn gwamnatin kasar na yanzu. Don haka ne a shekaran da ta gabata aka yi ta samun tashe tashen hankula a yankin.