Libya: An Kawo Karshen Aikin Soja Na Tsarkake Birnin Benghazi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i26931-libya_an_kawo_karshen_aikin_soja_na_tsarkake_birnin_benghazi
Dakarun tsaron Libiya sun sanar da cewa sun kawo karshen ayyukan su na tsarkake birnin Benghazi dake gabashin kasar daga kungiyoyin 'yan ta'adda.
(last modified 2018-08-22T11:31:14+00:00 )
Jan 02, 2018 06:28 UTC
  • Libya: An Kawo Karshen Aikin Soja Na Tsarkake Birnin Benghazi

Dakarun tsaron Libiya sun sanar da cewa sun kawo karshen ayyukan su na tsarkake birnin Benghazi dake gabashin kasar daga kungiyoyin 'yan ta'adda.

Wata majiyar soja daga gabashin Libiya ta tabbatar da cewa Rundunar tsaro ta musaman a ranar Litinin ta kawo karshen dukkanin ayyukanta na tsarkake birnin Benghazii daga kungiyoyin 'yan ta'adda.

Rahoton ya ce bayan fitar da mayakan 'yan ta'addar a birnin,  a halin yanzu an fara samun kwanciyar hanakali a birnin.

Majiyar da ta bukaci kada a bayyana sunanta, ta ce a karshen ayyukan na dakarun tsaro a birnin Benghazi, an hallaka 'yan ta'adda biyar sannan kuma an gano wasu gawawwaki na 'yan ta'addar da suka hallaka a yayin musayar wuta tsakanin su da sojoji.

Boren da al'ummar kasar Libiya suka yi a shekarar 2011 kan gwamnatin marigayi kanal Mu'amar Gaddafi, daga birnin Benghazi ne aka fara shi, garin dake a matsayin babban birni  na biyu a kasar ta Libiya cikin shekaru uku da suka gabata ya kasance filin daga tsakanin dakarun dake biyayya da Khalifa Haftar da kungiyoyin 'yan ta'adda da suka mamaye birnin.