Wasu Gungun 'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Kudancin Najeriya
Jami'an 'yan sandan Najeriya sun sanar da kai harin wani gungun 'yan bindiga kan mabiya kirista a kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa wasu yan binduga da ba a gane ko su waye ba a garin Omoku da ke jihar Rivers sun bude wuta kan wasu tarin Jama'a da suka hada da maza da mata har da kananan yara, da suka fito daga coci-coci, inda kawo yanzu aka tabbatar da mutuwar mutane 35.
Wadanda suka rasa rayukannasu dai, suna dawowa ne daga taron ibada da kuma bikin Cross Over Night,wato taron tsallakawa daga shekara ta 2017 Zuwa 2018, da ya gudana a Coci Coci daban-daban a garin na omoku.
Har kawo yanzu dai, rundunar 'yan sandan jihar ta Rivers ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin kafin ta yi cikakken bayani kan zahairin abin da a afku.
Jihar Rives na da muhiman rijiyoyin man fetir, to sai dai wasu daga cikin al'ummar jihar na kokawa kan halin ko in kula daga bangaren gwamnatin tarayya kan wasu abubuwan da suke bukatar a mayar da hankali a kansu a jahar.