Shugaban Mali Na Shirin Yi Wa 'Yan Tawayen Kasar Afuwa
(last modified Tue, 02 Jan 2018 17:12:22 GMT )
Jan 02, 2018 17:12 UTC
  • Shugaban Mali Na Shirin Yi Wa 'Yan Tawayen Kasar Afuwa

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya sanar da cewa nan gaba kadan za a kafa wata doka a kasar da za ta yi afuwa ga 'yan tawayen da suka shiga cikin rikicin shekara ta 2012 a kasar afuwa.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya jiyo shugaban kasar Malin yana fadin cewa manufar dokar ita ce tabbarar da sulhu ta kasa da kuma tabbatar da hadin kai tsakanin al'ummar kasar.

Shugaba Keita ya kara da cewa ana ci gaba da rubuta kundin kudurin dokar wacce ta kumshi yin afuwa ga dukkanin 'yan tawayen da suka dau makami amma ban da wadanda suka zubar da jinin mutane, kamar yadda kuma ya sanar da shirin da gwamnatin ta sa take da shi na dawo da dukkanin 'yan tawayen da suke dau makami din cikin al'umma amma da sharadin sun ajiye makamansu da kuma yin watsi da duk wani tashin hankali.

A watan Maris na shekara ta 2012 ne 'yan tawayen a arewacin kasar suka kaddamar da shirin su na tawaye da kuma daukar makami lamarin da ya share fagen shigowar kungiyoyin 'yan ta'adda kasar.