Kungiyar Tarayyar Afirka Na Shirin Kafa Wani Sansanin Soji A Kasar Kamaru
Ministan tsaron kasar Kamaru, Joseph Beti Assomo, ya sanar da cewa kungiyar Tarayyar Afirka za ta kafa wani sansani na sojojin kai dauki na kungiyar a kasar Kamaru.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar ministan tsaron kasar Kamarun, Joseph Beti Assomo, ya sanar da hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a lokacin da ake bikin share fagen bude sansanin sojin da aka gudanar a birnin Douala da ke yammacin kasar karkashin jagorancin firayi ministan kasar Philémon Yang.
Mr. Asomo ya ce sansanin wanda za a kafa shi a birnin na Douala zai kumshi rumbuna na makamai da sauran kayayyakin ayyukan soji don saukake wa sojojin Tarayyar Afirkan saukin samun kayyayakin da suke a yayin gudanar da ayyukansu na tabbatar da zaman lafiya a nahiyar Afirkan.
Tun shekaru 15 da suka gabata ne dai aka fara maganar kafa wannan sansanin, to sa idai kuma matsalolin da aka fuskanta musamman na kudi sun hana tabbatuwar hakan.