Janar Khalifa Haftar Ya Jaddada Muhimmancin Gudanar Da Zabuka A Kasar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27135-janar_khalifa_haftar_ya_jaddada_muhimmancin_gudanar_da_zabuka_a_kasar_libiya
Babban kwamnadar rundunar sojin Libiya da ke gabashin kasar Janar Khalifa Haftar ya jaddada muhimmancin gudanar da zabukan 'yan Majalisun Dokokin Libiya bayan gudanar da dukkanin shirye-shiryen da suka dace.
(last modified 2018-08-22T11:31:15+00:00 )
Jan 09, 2018 06:32 UTC
  • Janar Khalifa Haftar Ya Jaddada Muhimmancin Gudanar Da Zabuka A Kasar Libiya

Babban kwamnadar rundunar sojin Libiya da ke gabashin kasar Janar Khalifa Haftar ya jaddada muhimmancin gudanar da zabukan 'yan Majalisun Dokokin Libiya bayan gudanar da dukkanin shirye-shiryen da suka dace.

A jawabinsa kan bukatar gudanar da zabuka a Libiya: Babban kwamandan rundunar sojin Libiya da ke gabashin kasar Janar Khalifa Haftar ya bayyana cewa: Dole ne kafin batun gudanar da zabukan 'yan Majalisun Dokokin Kasar a samu daidaiton baki a tsakanin jami'an Libiya kan kundin tsarin mulkin kasar.

Khalifa Haftar ya kara da cewa: Samun daidaito baki a tsakanin jami'an Libiya shi ne matakin farko da zai kawo karshen duk wasu tashe-tashen hankula da suke kai ga zubar da jini a kasar.

Tun a shekara ta 2011 Libiya ta tsunduma cikin rikicin yake-yake tsakanin kungiyoyi bayan da kasashen yammacin Turai da Amurka suka kaddamar da yaki kan kasar tare da kashe shugabanta Mu'ammar Gaddafi, inda a halin yanzu ake da gwamnatoci biyu a kasar ta Libiya.