An Kama Yan Ta'adda Da Dama A Kasar Mali
Majiyar sojojin kasra Faransa wadanda suke aikin tabbatar da zaman lafiya a arewacin kasar Mali ta bada labarin kama gungun yan ta'adda dauke da makamai a yankin arewa maso gabacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto majiyar rundunar sojojin kasar Faransa wacce ake kira Barkhan, wacce kuma take aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar Mali tana cewa da gano makamai masu yawa, da kayan aikin soje a garin Menaka dake arewa maso gabacin kasar Mali a lokacinda suke bincike a ranakun 10 da 11 na watan Jeneru da muke ciki.
Labarin ya kara da cewa rundunar ta kama wasu daga cikin yayan kungiyoyin yan ta'adda masu kafirta mutane a garin.
Sai dai wata majiyar hukumomi a garin Menaka tace, mutanen da sojojin Faransa suka kama ba yan ta'adda bane.
Rundunar sojojin Faransa ta Barkhan dai ta kunshi sojoji 4000 wadanda aka rarrabasu a cikin kasashe biyar na yankin Sahel, wadanda suka hada da Mali, Niger, Chadi, Borkina Faso da kuma Mauritania.