An Kaiwa Sojojin Faransa Hari A Mali
An kai harin Bam kan tawagar sojojin kasar Faransa a kasar Mali
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Ma'aikatan hadin gwiwa na sojojin Faransa a yau juma'a na cewa wani Bam da aka dasa a hanyar Dakarun kasar Faransa ya tashi da wani motar sojan kasar a tsakanin hanyar garin Ménaka da Indelimane a gabashin kasar ta Mali, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar sojojin kasar ta Faransa uku.
Sanarwa ta ce harin na ta'addanci ne kuma ya faru ne ranar Alhamis 11 ga watan janairun da muke ciki a yayin tunin da zagayowar ranar da Sojojin kasar Faransa suka fara kai farmaki kan 'yan ta'adda a kasar ta Mali a shekarar 2013 da ake kira da ranar Serval, daga wannan lokaci zuwa yanzu Sojojin Faransa 18 ne suka rasa rayukansu a kasar ta Mali.
Tun bayan da Sojoji suka kifar da Gwamnati shekarar 2012 a kasar ta Mali, wasu kungoyoyi suka dauki makamai a arewacin kasar, a farkon shekarar 2013 ne Sojojin kasar Faransa da MDD suka shiga kasar ta Mali domin taimakawa sojojin kasar na fatattakar 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayin addini da suka mamaye wasu yankunan arewacin kasar.