An Sace Ma'aikatan MDD Uku A Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27259-an_sace_ma'aikatan_mdd_uku_a_libiya
Majiyar tsaron Libiya ta sanar da sace wasu ma'aikatan Majalisar dinkin duniya guda uku a kasar .
(last modified 2018-08-22T11:31:17+00:00 )
Jan 14, 2018 06:26 UTC
  • An Sace Ma'aikatan MDD Uku A Libiya

Majiyar tsaron Libiya ta sanar da sace wasu ma'aikatan Majalisar dinkin duniya guda uku a kasar .

Kafar watsa labaran Bawabatu-Ifrikiya-al-ahbariya ta nakalto majiyar tsaron Libiya a jiya Asabar na cewa wasu gungun 'yan bindiga sun yi awon gaba da ma'aikatan MDD na bangaren kula da 'yan gudun hijra  uku yayin da suka bar birnin Tripoli a kan hanyar su ta zuwa birnin al Shati na kusa da garin Sabha dake kudancin kasar.

Al- Saadi Mohammad Ali Shugaban hukumar 'yan sanda na yankin Sabha ya bayyana cewa an gano biyu daga cikin wadanda aka sacen a wata unguwa a garin Sabha, kuma a halin da ake ciki, ana ci gaba da tattaunawa da shugabanin kabilu domin gano mutum na uku.

Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta MDD na gudanar da ayyukanta ne na kokarin taimakawa bakin haure masu son zuwa kasashen turai da kuma suke fuskantar matsalolin rayuwa da cin zarafi a kasar ta Libiya komawa kasashen su na asali.

Kasar Libiya dai ta fada cikin rikici tun bayan da aka kifar da gwamnatin kanal Mu'amar Ghaddafi a shekarar 2011.