Shugaban Tunisiya Ya Gana Da Shugabanin Siyasa Kan Halin Da Kasar Ciki
(last modified Sun, 14 Jan 2018 06:28:32 GMT )
Jan 14, 2018 06:28 UTC
  • Shugaban Tunisiya Ya Gana Da Shugabanin Siyasa Kan Halin Da Kasar Ciki

Shugaban kasar Tunisiya Beji Caid Essebsi ya tattaunawa dashugabanin jam'iyun siyasa da kungiyoyin fararen hula a wani mataki na kwantar da zanga-zangar adawa da tsarin gwamnati.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa  a jiya Asabar Shugaban kasar Tunisiya ya gana da shugabanin siyasa da na kungiyoyin farar hula, inda suka kwashe sama da sa'o'i biyu ana tattaunawa na yadda za a fitar da kasar daga cikin halin da take ciki na bore.

Rachid Gannushi, shugaban kungiyar Annahda ta ya ce sun gabatar da shawarwari na fitar da kasar daga cikin wannan yanayi, sai dai bai yi karin haske ba a game da shawarwarin da suka gabatar.

A wannan Lahadi ce, kasar ta Tuninsiya ke cika shekaru bakwai da kawo karshen mulkin kama karya, inda a kowace shekara 'yan kasar ke bikin nasarar da suka samu ta juyin juya hali a kasar, to amma shekarar ta bana ta zo wa 'yan kasar cikin wani yanayi na zanga-zangar adawa da karin haraji wanda hakan ya sanya farashin kayar masarufi ya karu.