MDD Za Ta Binciki Jirgin Ruwa Mai Makare Da Abubuwan Fashewa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27295-mdd_za_ta_binciki_jirgin_ruwa_mai_makare_da_abubuwan_fashewa
Manzon mUsamman na MDD a kasar Libya, Gassan Salamah, ya ce; Majalisar za ta aike da kwararru domin yin bincike akan jirgin ruwan kasar Turkiya mai makare da abubuwa masu fashewa
(last modified 2018-08-22T11:31:17+00:00 )
Jan 15, 2018 11:49 UTC
  • MDD Za Ta Binciki Jirgin Ruwa Mai Makare Da Abubuwan Fashewa

Manzon mUsamman na MDD a kasar Libya, Gassan Salamah, ya ce; Majalisar za ta aike da kwararru domin yin bincike akan jirgin ruwan kasar Turkiya mai makare da abubuwa masu fashewa

Gassan Salamah wanda ya yi  rubutu a shafinsa na Twitter ya ci gaba da cewa; Kasar Libya tana da bukatuwa da zaman lafiya da tsaro, kuma da akwai kudurin Majalisar Dinkin Duniya wanda ya hana shigar da makamai kasar.

A ranar asabar da ta gabata ne dai gwamnatin kasar Girka ta sanar da tsaida wani jirgin ruwa mai suna " Anmakare"  da abubuwa masu fashewa wanda kuma mallakin kasar Turkiya ne.

Sai dai ofishin jakadancin kasar Turkiya da yake a kasar Libya ya ce; makaman da suke cikin jirgin mallakin kasar Habasha ne ba Libya ba.