Libya: An Kame Wani Dan Kasar Masar Mai Alaka Da Da'esh
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27339-libya_an_kame_wani_dan_kasar_masar_mai_alaka_da_da'esh
Majiyar watsa labaru mai alaka da gwamnatin hadin kan kasar Libya ta ce; An kama mutumin ne agari Sart, bisa zargin yana safarar 'yan kungiyar Da'esh zuwa kadancin kasar
(last modified 2018-08-22T11:31:17+00:00 )
Jan 16, 2018 18:52 UTC
  • Libya: An Kame Wani Dan Kasar Masar Mai Alaka Da Da'esh

Majiyar watsa labaru mai alaka da gwamnatin hadin kan kasar Libya ta ce; An kama mutumin ne agari Sart, bisa zargin yana safarar 'yan kungiyar Da'esh zuwa kadancin kasar

Sanarwar ta ci gaba da cewa;; Tuni mutumin ya yi furuci da laifin da yake aikatawa na safarar 'yan ta'addar.

Tun a 2011 ne garin na Sart ya zama cibiyar kungiyoyin 'yan ta'adda wanda daga baya Da'esh ta sami gindin zama a cikinsa. A cikin watan Disamba na 2016 ne sojojin da suke a karkashin janar Halifa Haftar suka kakkabe 'yan Da'esh daga cikin garin.

Tun bayan kifar da gwamnati Khaddafi a 2011 ne Libya ta fada cikin hargitsi da rashin tsayayyar gwamnati.