MDD Ta Damu Da Tisa Keyar 'Yan a Waren Kamaru Daga Najeriya
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (HCR) ta nuna matukar damuwa dangane da matakin mahukuntan Najeriya na tisa keyar 'yan a waren Kamaru zuwa birnin Yaoude.
A sanarwar da ta fitar yau Alhamis hukumar ta HCR ta ce babban abun damuwa ne tisa keyar mutanen su 47 da karfin tsiya daga Najeriya zuwa Kamaru .
Hukumar ta ce galibin mutanen masu bukatar mafaka ne, wanda tisa keyarsu ya sabawa dokar kare 'yan gudun hijira ta kasa da kasa.
A ranar 26 ga watan Janairun da mukayi ban kwana da shi ne hukumar leken asiri ta Najeriya ta mikawa Kamaru mutanen da suka hada da jagoran 'yan fafatukar a ware na yankin masu magana da harshen turancin Ingilishi, wadanda gwamnatin Kamaru ke dangatawa da 'yan ta'adda.
Dama kafin hakan kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta yi gargadi akan tisa keyar mutanen zuwa Kamaru daga Najeriya, inda ta ce zasu fuskanci barazana da muzguna, sannan ba'a masu adalci a shari'a ba.