Libiya : Bakin Haure 10 Suka Suka Mutu A Teku
(last modified Sat, 03 Feb 2018 06:26:35 GMT )
Feb 03, 2018 06:26 UTC
  • Libiya : Bakin Haure 10 Suka Suka Mutu A Teku

Rahotanni daga Libiya na cewa bakin haure a kalla goma ne suka gamu da ajalinsu a yayin da kwale-kwalen dake dauke dasu ya nutse a teku akan hanyarsu ta zuwa Turai.

Wakiliyar hukumar kula da harkokin bakin haure ta MDD, IOM, a kasar Libiya Olivia Headon, ta ce an samu gawawwakin wasu mutane 10 da ruwa ya turo bakin gabar tekun, ciki hadda na 'yan Libiya 2 da kuma wasu 'yan kasar Pakistan su 8.

Hukumonin LIbiya sun ce ba'a cika samun 'yan kasar dake irin wannan tafiya ba ta barauniyar hanya zuwa kudancin turai.

A jiya ne dai hukumar kula da harkokin bakin haure ta MDD, IOM, ta ce ta samu rahoton mutuwar wasu 'yan ci rani da yawan su ya kai a kalla 90, bayan da kwale kwalen da suke ciki ya nutse a kusa da gabar ruwan kasar Libiya da sanyin safiyar Juma'a.

Hukumar IOM ta ce tana ci gaba da bincike, domin samun cikakkun bayanai game da aukuwar hadarin, tare da duba yiwuwar tallafa wa wadanda suka tsira.