Ziyarar Shugaban Kasar Faransa Zuwa Afirka
Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya kai ziyara kasashen Tunusiya da Senegal, inda ya tattauna tare da hukumomin kasar kan muhimman batutuwa daban daban, daga ciki akwai fadada alakar difulomasiya a tsakanin bangarorin biyu, yaki da ta'addanci da kuma batutuwan da suka shafi kasar Libiya.
A wani taron manema labarai da suka gudanar, shugaban kasar Faransa ya bayyana cewa ta'addanci shi ne tushen barazana a tsakanin kasashen biyu, domin haka yana da muhimmancin gaske kasashen biyu su hada karfi da karfe domin yakar sa. Har ila yau Shugaba Macron ya tabbatar da muhimmancin yin aiki tare a bangarori daban daban, inda suka sanya hannu kan wasu kudurori guda takwas.
Ziyarar shugaba Macron a Tunusiya na zuwa ne a yayin da kasar ke cikin matsalar tattalin arziki da zamantakewa bayan kwashe shekaru bakwai da juyin juya hali, inda a cikin makonin da suka gabata al'ummar kasar suka gudanar da zanga-zangar adawa dangane da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, rashin aikin yi da talauci da ya addabi matasan kasar.
A cikin irin wannan yanayi, ziyarar shugaban kasar Faransan nada muhimmanci a wajen hukumomin kasar ta Tunusiya, inda suka bayyana fatansu na ganin cewa ya janyo hankalin masu zuba jari na kasar Faransa su zuba hanun jarinsu a kasar da hakan na iya magance wasu matsalolin da kasar ke fuskanta, duk da wannan fata, amma babu wani abin a zo a gani da zai iya tasiri a tattalin arzikin kasar Tunusiya da aka cimma tsakanin kasashen biyu,a cewar masana, ci gaba da tayar da tarzoma, da ya yi sanadiyar rashin tsaro da kwanciyar hankali, na daga cikin dalilan da suka hana sanya hanun jari ga 'yan kasar Faransar a Tunusiya.
Abdulwahab Takiyat wani masanin tattalin arzikin kasar Tunusiya a wannan fage ya bayyana cewa, masu saka hanun jari, suna cewa yanayin tarzoma da rashin tsaro da kasar Tunusiya ke fama da su a yanzu, ba lokaci ne da ya dace na zuba hanun jari a kasar ba, domin haka fatan da wasu ke da shi na ganin 'yan kasar Faransa sun zuba hanun jari a kasar, fata ne da ba zai tabbata a halin yanzu ba.
A halin da ake ciki dai kasar Tunusiya na matukar bukatar masu zuba hanun jari domin fita daga cikin matsin tattalin arziki da take ciki, to amma ziyarar da shugaban kasar Faransa babu wani amfani na a zo gani da kasar ta Tunusiya za ta samu, inda masu sharhi ke ganin cewa ziyarar ta Macron, ziyara ce da tafi mayar da hankali kan harakokin siyasa.
Bayan kasar Tunusiya, Shugaba Macron ya yada zango a kasar Senegal, inda ya gana da shugaban kasar Macky Sall, inda suka cimma matsaya a kan fadada alaka a bangarori daban daban da suka shafi tattalin arziki da siyasa, daga cikin muhimman batutuwan da suka cimma har da sayen jiragen sama daga kasar ta Faransa, sannan kasar ta Faransa ta yi alkawarin bayar da kashi 10% na kasafin kudi na bangaren ilimi ga kasashen Afirka, sannan kuma daga karshe ya gana da 'yan kasarsa dake kasar ta Senegal.
A jumlace ana iya cewa hukumomin kasar Faransa na kokarin kara samun wurin zama ne a kasashen Afirka, bayan tunkarar abokan hamayar su a bagaren tattalin arziki da siyasa, kasar ta Faransa na bayan manufofi guda biyu ne a kasashen na Afirka, na farko hana kwararar bakin haure da kuma wanzuwar 'yan ta'adda a kasashen Turai, domin cimma wannan manufa kasar ta Faransa na matukar bukatar hadin kan shugabanin Afirka, wanda hakan ne ya sanya shugaban kasar ta Faransa ke ci gaba da kai kawo domin samun wannan hadin kai.