Yan Bindiga Sun Kashe Fararen Hula 4 A Yankin Arewacin Kasar Mali
Rundunar sojin Mali ta sanar da cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kashe fararen hula 4 a yankin da ke arewacin kasar.
A sanarwar da rundunar sojin Mali ta fitar a jiya Lahadi yana dauke da cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan yankin Talataye da ke garin Gao a shiyar arewa maso gabashin kasar, inda suka kashe fararen hula hudu.
Har ila yau sanarwar ta kara da cewa: A samamen da rundunar sojin kasar ta Mali take gudanarwa a shiyar arewa maso gabashin kasar, a cikin makon da ya gabata ta yi nasarar kashe 'yan ta'adda masu tarin yawa.
Rundunar sojin Mali ta daura alhakin kashe-kashen gillar da ake yi wa fararen hula a yankin arewa maso gabashin kasar kan mayakan 'yan aware da suka yi kokarin kafa kasar Azawad a yankin arewacin kasar ta Mali.