An Kashe 'Yan Kunar Bakin Wake Biyu A Kamaru
Majiyar tsaron Kamaru ta sanar da kisan 'yan kunar bakin wake biyu da ake zaton 'yan boko haram ne a yankin Kordo dake arewacin kasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar Rundunar tsaron kasar kamaru ta sanar da cewa sojojin kasar sun hallaka wasu mutane biyu da ake kyautata zaton 'yan boko haram ne a yayin da suka kokarin kai harin kunar bakin wake a kauyen Kordo dake arewacin kasar.
Rahoton ya ce jami'an tsaron sun cabke wani dan kunar bakin waken na daban,to saidai bayan a kame shin, bom din da ya yi jigida da shi ya tarwatsa, inda ya hallaka shi tare kuma da jikkata wasu jami'an tsaro da dama.
Kauyen Kordo, na kai iyakar kasar ta kamaru da Najeirya, inda a cikin shekarun baya bayan nan ya fuskanci hare-haren ta'addanci na kungiyar boko haram.