An Karfafa Matakan Tsaro A Garin Bangazi Na Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28137-an_karfafa_matakan_tsaro_a_garin_bangazi_na_libiya
Hukumomin tsaron garin Bangazi na gbashin kasar Libiya sun kara karfafa matakan tsaro domin kalubalantar barazanar 'yan ta'adda a garin.
(last modified 2018-08-22T11:31:25+00:00 )
Feb 12, 2018 11:45 UTC
  • An Karfafa Matakan Tsaro A Garin Bangazi Na Libiya

Hukumomin tsaron garin Bangazi na gbashin kasar Libiya sun kara karfafa matakan tsaro domin kalubalantar barazanar 'yan ta'adda a garin.

Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto hukumomin tsaron Bangazi na cewa sun dauki wannan mataki ne bayan wani taron gaggauwa da aka gudanar na wsu manyan jami'an tsaron kasar tare da halartar Piraministan kasar na ficin gadi.

hukumomin tsaron birnin Bangazin sun sanar da cewa kungiyoyin 'yan ta'adda na kokarin kai hare-haren ta'addanci da kuma tayar da bama-bamai a jahar

A makonni biyu da suka gabata, an kai harin ta'addanci a daya daga cikin masallatan birnin Bangazi, tare da hallaka Mutane 34 yayin da wasu sama da 100 na daban suka jikkata, har ya zuwa yanzu babu wata kungiya ko wani mutum da ya dauki alhakin kai harin.