Kamaru: 'Yan Aware Sun Yi Awon Gaba Da Wani Jami'in Gwamnati
(last modified Tue, 13 Feb 2018 12:21:27 GMT )
Feb 13, 2018 12:21 UTC
  • Kamaru: 'Yan Aware Sun Yi Awon Gaba Da Wani Jami'in Gwamnati

Kakakin dakarun tsaron kasar Kamaru sun sanar da cewa 'yan aware sun sace wani jami'in gwamnati a yankin.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto  Didier Bajak mai magana da yawun dakarun tsaron kamaru  a jiya Litinin na cewa 'yan aware sun yi awan gaba da shugaban yankin masu magana da yarar inglishi wato Batibo dake arewa maso yammacin kasar.

Bajak ya ce dakarun sojin da 'yan sandar kasar sun fara gudanar da bincike tun a daren jiya Litinin domin gano jami'in, amma har yanzu ba a kai ga gano shi ba, an sace jami'in ne a yayin da ake gudanar da bikin hadewar kasar wuri guda karo na 52 wanda aka bashi taken bikin Matasa.

Tuni masu fafukar ballewa daga kasar ta Kamaru suka dauki alhakin sake jami'in, 

Tun a watan watan Oktoban shekarar da ta gabata ce yankunan masu amfani da harshen inglishi na arewa maso gabashin kasar ta kamaru ya fada cikin rikici, bayan da wasu al'ummar yankin suka shelanta ballewa daga kasar, kuma ya zuwa yuanzu rikicin ya ci rayukan jami'an tsaro 26.