Libya: 'Yan Ci-Rani Fiye Da 30 Sun Halaka Sanadiyyar Hatsarin Mota
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28215-libya_'yan_ci_rani_fiye_da_30_sun_halaka_sanadiyyar_hatsarin_mota
Tashar talabijin din alhadath ta kasar Libya ce ta ba da labarin mutuwar mutanen 30 sanadiyyar hatsarin da motar da take dauke da su ta yi.
(last modified 2018-08-22T11:31:25+00:00 )
Feb 14, 2018 19:02 UTC
  • Libya: 'Yan Ci-Rani Fiye Da 30 Sun Halaka Sanadiyyar Hatsarin Mota

Tashar talabijin din alhadath ta kasar Libya ce ta ba da labarin mutuwar mutanen 30 sanadiyyar hatsarin da motar da take dauke da su ta yi.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan kasar da 'yan ci-ranin su ka fito.

Kasar Libya wacce take a matsayin hanyar wucewar 'yan ci-rani zuwa turai, ta zama wurin da suke yawan mutuwa ko a kan doron ruwa ko kuma ta fataucinsu da ake yi, da sayar da su a matsayin bayi a kasuwa.

A kowace shekara ta Allah, dubban 'yan ci-rani ne su ke rasa rayukansu a cikin kasar ta Libya.