An Sauke Ministan Cikin Gidan Libiya Daga Mukaminsa
Majalisar Shugabancin kasar Libiya ta dakatar da Aref Al-Khouja ministan cikin gidan kasar daga kan mukaminsa.
Kamfanin dillancin labaran Iran ya habarta cewa a daren jiya Alhamis, majalisar shugabancin kasar Libiya ta sauke Aref Al-Khouja ministan cikin gidan kasar daga kan mukaminsa tare da maye gurbinsa da Abdelsalam Mustafa Ashor.
Wannan dai shi ne karo na farko da Majalisar shugabancin kasar ta Libiya ta yi wa gwamnatin kasar garan bawul.
A ranar 17 ga watan janairun da ya gabata ce, majalisar shugabancin kasar ta Libiya ta sanar da cewa za ta gudanar da sauyi a cikin majalisar.
Tun a shekarar 2011 ne kasar ta Libiya ta fada cikin rikici, bayan da al'ummar kasar tare da goyon bayan kasashen Turai da Amirka suka kifar da gwamnatin marigayyi Kanal Mu'ammar Kaddafi.