An Bukaci Dakatar Da Kai Hare-Hare A Arewacin Siriya
Ministan harakokin wajen Jamus ya bukaci a dakatar da duk wani motsin soja a arewacin kasar Siriya
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Sigmar Gabriel ministan harakokin wajen kasar Jamus yayin taron ministocin harakokin wajen kasashen Turai da ya gudana a birnin Sofia na kasar Bulgaria a jiya Alhamis na cewa ya kamata a tabbatar an koma kan tebirin tattaunawa tsakanin gwamnatin Siriya da kuma kungiyoyin dake dauke da makamai sannan kuma a dakatar da duk hare-haren da ake kaiwa a arewacin kasar.
A nasa bangare, ministan harakokin wajen kasar Faransa Jean-Yves Le Drian ya bayyana cewa wajibi a gaggauta komawa kan tebirin tattaunawa tsakanin 'yan kasar ta Siriya bisa goyon Majalisar Dinkin Duniya.
A jiya Alhamis ne ministocin harakokin kasashen wajen Turai suka fara gudanar da taro domin tattauwa halin da kasar siriya ke ciki, musaman ma a game da yadda hukumomin kasar turkiya suka kaddamar da hare-haren kan al'ummar kurdayan kasar ta siriya a cikin 'yan kwanakin nan.
A yau juma'a ce ake san za a kamala wannan taro.