Piraministan Libiya:Shigar 'Yan Kasashen Waje Shi Ke Kara Dagula Al'amura
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28331-piraministan_libiya_shigar_'yan_kasashen_waje_shi_ke_kara_dagula_al'amura
Piraministan kasar Libiya ya bayyana cewa shigar 'yan kasashen waje shi ke kara tsananta sabani a tsakanin 'yan kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:26+00:00 )
Feb 18, 2018 15:58 UTC
  • Piraministan Libiya:Shigar 'Yan Kasashen Waje Shi Ke Kara Dagula Al'amura

Piraministan kasar Libiya ya bayyana cewa shigar 'yan kasashen waje shi ke kara tsananta sabani a tsakanin 'yan kasar.

Tashar talabijin din Aljazeera ta habarta cewa Dubun dubatan mutanen kasar Libiya ne suka gudanar da gangami da jerin gwano don tunawa da shekaru 7 da yunkurin da suka gudanar da yayi sanadiyyar kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Kanar Mu'ammar Gaddafi, duk kuwa da matsalolin tsaro da kasar ta fada bayan kifar da gwamnatin.

A yayin wannan taro, Piraministan kasar Fayez al-Sarraj ya yi kakkausar suka kan yadda wasu kasashen waje ke yin katsa landan a harakokin cikin gidan kasar, inda irin katsa landan da wasu kasashen waje ke yi a harakokin cikin gidan kasar shi ke kara tsananta sabani a tsakanin al'ummar kasar Libiya.

Al-sarraj ya bukaci 'yan majajalisun kasar da su gaggauta kada kuri'a a kan sabon kundin tsarin kasar tare da tabbatar da cewa a halin yanzu abinda zai fidda kasar nan daga cikin halin da take ciki, da kuma sasantawa tsakanin al'ummar kasar shi ne babban abinda gwamnati ta sanya a gaba.