Al'ummar Tunusiya Suna Ci Gaba Da Zanga-Zangar Nuna Kiyayya Ga H.K.Isra'ila
Al'ummar Tunusiya suna ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman kafa dokar da zata haramta kulla duk wata alakar jakadanci tsakanin kasar ta Tunusiya da Haramtacciyar kasar Isra'ila.
Daruruwan al'ummar Tunusiya sun gudanar da zanga-zanga gami da taron gangami a yau Litinin a matsayin rana ta biyu a jere a birnin Tunis fadar mulkin kasar suna neman Majalisar Dokokin Tunusiya da ta hanzarta kada kuri'ar amincewa da daftarin kudurin dokar da aka gabatar mata da ke neman haramta duk wani matakin kulla alakar jakadanci tsakanin kasar Tunusiya da Haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kungiyoyin kare hakkin bil-Adama da na fararen hulan kasar Tunusiya ne suke jagorantar gudanar da zanga-zangar da ke samun halattar daruruwan jama'a daga sassa daban dabanna kasar. Tun a watan Disamban shekarar da ta gabata ta 2017 ne wasu kungiyoyin kare hakkin bil-Adama da na fararen hula suka gabatar da wannan daftarin kudurin a gaban Majalisar Dokokin Tunusiya, inda a halin yanzu al'ummar kasar suke kokarin ganin an hanzarta kada kuri'ar amincewa da kuduri domin ya zame dokar kasar.