Yemen: An Halaka Sojojin Saudiyya Biyu
Feb 24, 2018 03:11 UTC
An kashe sojojin na Saudiyya biyu ne ta hanyar harbinsu daga nesa da wani kwararren maharbi na sojojin Yemen ya yi.
Majiyar sojan kasar Yemen ta fada da safiyar yau asabar cewa; an hallaka sojojin ne a cikin sansaninsu da yake a yankin Jizan.
Bugu da kari rundunar sa-kai ta "Ansarullah' sun kashe wasu karin Sojojin na Suadiyya a yankin na JIzan.
Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa bisa cikakken goyon bayan Amurka sun fara kai wa Yemen hari ne a 2015 tare da killace kasar ta sama da ruwa.
Ya zuwa yanzu fiye da mutane 13,000 ne suka muyu sanadiyyar hare-haren na Saudiyya.
Tags