Rikici Ya Hallaka Mutane 2 A Kudancin Kasar Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28541-rikici_ya_hallaka_mutane_2_a_kudancin_kasar_libiya
Hukumomin kasar Libiya sun sanar da mutuwar mutane biyu sanadiyar harin masu dauke da makamai a wani wurin binciken jami'an tsaro dake kudancin kasar
(last modified 2018-08-22T11:31:28+00:00 )
Feb 24, 2018 19:02 UTC
  • Rikici Ya Hallaka Mutane 2 A Kudancin Kasar Libiya

Hukumomin kasar Libiya sun sanar da mutuwar mutane biyu sanadiyar harin masu dauke da makamai a wani wurin binciken jami'an tsaro dake kudancin kasar

Cikin wata sanarwa da suka fitar a wannan asabar, hukumomin tsaron kasar Libiya sun bayyana cewa wasu gungun 'yan bindiga sun kai hari a wani wurin binciken 'yan sanda a kauyen Umu-Arnab dake yankin Marzok na kudancin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin kasar biyu tare da jikkata wasu da dama na daban.

Muhamad Jabir Saleh daya daga cikin manyan jami'an kasar ta Libiya ya bayyana cewa a yayin da maharan suka tunkari Sojojin kai tsaye sai suka buda wuta kansu sannan suka gudu, bayan haka, sai sojojin suka bi bayansu, inda suka biyu daga cikin su, dayan kuwa ya samu nasarar tserewa.

Sanarwar ta tabbatar da cewa dukkanin maharan 'yan kasshen waje ne.

A shekara ta 2011 ne dai al'ummar kasar Libiyan wadanda suke samun goyon bayan wasu kasashen larabawa da na yammaci suka kaddamar da wani yunkurin nuna rashin amincewa da gwamnatin marigayi Kanar Gaddafin lamarin da yayi sanadiyyar kifar da gwamnatin tasa da kuma kashe shi.