Kamaru: "Yan Aware Sun Sake Sace Wani Jami'in Gwamnati
(last modified Mon, 26 Feb 2018 19:06:48 GMT )
Feb 26, 2018 19:06 UTC
  • Kamaru:

Kamfanin dillancin labarin Xinhua ya ambato majiyar gwamnatin kasar tana cewa; 'Yan awaren sun sace Nimboum Arung Jung wanda jami'i na al'amurran zamantakewa a yankin arewa maso gabacin kasar.

Majiyar ta kara da cewa kawo ya zuwa yanzu jami'an gwamnatin yankin da aka sace sun kai biyu. A ranar 11 ga watan Febrairu ma, 'yan awaren sun sace Batibo wanda shi ma jami'in gwamnati ne a yankin masu magana da harshen Ingilishi.

Yankin da ke magana da turanci a arewa masu yammacin kasar ta Kamaru, sun shelanta kudurinsu na ballewa daga kasar domin kafa tasu kasar.

Adadin masu magana da harshen na turanci sun kai kaso 20% na jumillar al'ummar kasar mai mutane miliyan 20.