Mali : Bom Ya Kashe Jami'an Wanzar Da Zaman Lafiya Na MDD 4
Mar 01, 2018 11:17 UTC
Majalisar Dinikin Duniya ta tabbatar da mutuwar wasu jami'an na kiyaye zaman lafiya hudu a Mali, a lokacin da motarsu ta taka wasu boma-bomai.
Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya bayyana cewa, jami'an sun rasa rayukansu ne a yayin da motarsu ta taka wasu ababe masu fashewa a gefen hanya a garin Boni-Douentza dake yankin Mopti, kana wasu hudu na daban suka jikkata.
Babban sakatare na MDD, ANtonio Guteress yayi Allah wadai da harin, tare da jaddada cewa hari kan jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD, na zaman laifukan yaki ne.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba jami'an MDD ke rasa rayukansu a cikin irin wannan yanayi ba.
Tags