Gwamnatin Libiya Ta Bukaci Dakatar Da Bude Wuta A Yankin Kudancin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28707-gwamnatin_libiya_ta_bukaci_dakatar_da_bude_wuta_a_yankin_kudancin_kasar
Gwamnatin hadin kan kasar Libiya ta bukaci hanzarta dakatar da bude wuta a garin Sabha da ke kudancin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:31:30+00:00 )
Mar 02, 2018 11:59 UTC
  • Gwamnatin Libiya Ta Bukaci Dakatar Da Bude Wuta A Yankin Kudancin Kasar

Gwamnatin hadin kan kasar Libiya ta bukaci hanzarta dakatar da bude wuta a garin Sabha da ke kudancin kasar.

Gwamnatin hadin kan kasa a Libiya ta bukaci hanzarta daukan matakan shawo kan rikicin da ya kunno kai tsakanin bangarori biyu da suke dauke da makamai a garin Sabha da ke kudancin Libiya da nufin kare karukan mutane musamman fararen hula.

Rahotonni sun bayyana cewa tun a makon da ya gabata ne aka samu bullar rikici a tsakanin sojojin da suke biyayya ga gwamnatin hadin kan kasar da ke birnin Tripoli da kuma sojojin da suke goyon bayan Janar Khalifa Haftar babban kwamandan sojin kasar da ke da matsuguni a garin Tobruk a gabashin kasar ta Libiya, inda aka samu hasarar rayukan mutane akalla hudu tare da jikkatan wasu na daban.