Kungiyar G5 Sahel Ta Yi Tir Da Harin Burkina Faso
Shugaba Isufu Mahamadu na Jamhuriya Nijar, kana shugaban kungiyar kasashen gungun G5 Sahel, ya yi tir da allawadai da jerin hare haren ta'addancin da wasu 'yan bindiga suka kai a birnin Ouagadugu na kasar Burkina Faso a jiya Juma' a.
A wata sanarwa da ofishin shuwagabancin kungiyar ya fitar, Shugaba Isufu ya jinjina wa dakarun kasar ta Burkina Faso akan kokarin da suka wajen murkushe 'yan ta' addan cikin takaitacen lokaci.
A hannu daya kuma sanarwar ta mika sakon ta'azziya ga iyalan jami'an tsaro da suka rasa rayukansu da kuma fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata da kuma jajanta wa al'ummar ta Burkina Faso.
A kalla mutane 30 ne ciki har da jami'an tsaro suka rasa rayukansu a jerin hare haren da wasu 'yan bindiga suka kai a ofishin jakadancin Faransa da kuma hedikwatar tsaro a Ouagadugu babban birnin kasar ta Burkina Faso.
Har zuwa yau dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai harin.