Rawar H.K. 'Isra'ila' Wajen Dakile Zanga-Zangar Adawa Da Gwamnati Kamaru
Rahotanni sun bayyana cewar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta aike da sojoji da jami'an tsaronta da nufin taimakawa gwamnatin Paul Biya na kasar Kamaru wajen kawo karshen zanga-zangar kin jinin gwamnati da al'ummar kasar suke yi.
Kafar watsa labaran Al-Quds al-Arabi ta bayyana cewar shugaban kasar Kamarun, Paul Biya yana ci gaba da amfani da wasu jami'an tsaron HKI da kuma wasu jami'an tsaron kasar Kamarun da suka sami horarwa ta musamman a 'Isra'ilan' wajen ci gaba da diran mikiyan da yake yi wa masu adawa da gwamnatinsa tsawon shekara guda da rabin da ta gabata.
Rahotanni sun ce tun da jimawa ne dai shugaba Biyan ya aike da wadannan jami'an tsaron na sa zuwa HKI don samun horarwa ta musamman kan yadda za a kawo karshen duk wata zanga-zanga da kuma tarzomar da za a tayar don nuna adawa da siyasar gwamnatinsa.
Tun daga watan Oktoban 2016 ne dai kasar Kamarun take fuskantar rikici da rashin tabbas na siyasa musamman a yankunan da suke magana da harshen turancin Ingila da kuma wasu yankuna na daban na kasar don nuna rashin amincewa da siyasar shugaba Biya din inda jami'an tsaron gwamnatin suke ci gaba da dirar mikiya ga masu zanga-zangar.