An Ceto Bakin Haure 335 A Gabar Ruwan Libiya
(last modified Sun, 11 Mar 2018 05:52:43 GMT )
Mar 11, 2018 05:52 UTC
  • An Ceto Bakin Haure 335 A Gabar Ruwan Libiya

Jami'an tsaron gabar ruwan Libiya, sun yi nasara ceto bakin haure 335 a gabar ruwan yammacin kasar, a lokacin da suke kokarin tsallakawa Turai ba bisa ka'ida ba.

 An dai ceto bakin hauren ne gabar ruwa yankin Zaouïa, dake yammacin kasar ta Libiya, a nsian kilomita 45 daga yammacin Tripoli babban birnin kasar.

Da yake bayyana hakan, kakakin jami'an tsaron gabar ruwan ta Libiya, Ayob Qassem, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren Xinhua cewa, dukkan bakin hauren sun samu kula yadda ya kamata.  

Daga cikin bakin hauren da aka ceton da akwai yara bakwai, a cewar kakakn jami'an tsaron, saidai ba tare da bayyana ko an samu hassara rai ba ko kuma A'a.

Tun dai bayan faduwar gwamnatin tsohon shugaban kasar Libiya, Muammar Ghaddafi a cikin shekara 2011, matsalar kwararar bakin haure dake bi ta Libiya don wucewa Turai, ta dada tsananta.