'Yar Wasan Kasar Aljeriya Ta Ki Karawa Da 'Yan Wasan H.K.Isra'ila
A ci gaba da kyamar da ake nuna wa yahudawa 'yan mamaya, 'yan wasan kokawa na kasar Aljeriya sun ki amincewa su kara da 'yan wasan haramtacciyar kasar Isra'ila a gasar kokawar da ake yi a kasar Moroko.
Kamfanin dillancin labaran kasar Iran IRNA ya jiyo kafafen watsa labaran kasar Aljeriyan suna fadin cewa daya daga cikin 'yan wasan kokawa na kasar Aljeriyan da suke halarta gasan kokawa da ake gudanarwa a garin Agadir na kasar Morokon mai suna Amina Belghazi ta ki amincewa ta yi kokawa da daya daga cikin 'yan tawagar HK.Isra'la da aka hada su; lamarin da ya fuskanci jinjinawa daga 'yan kallo.
Rahotannin sun ce mafi yawa daga cikin 'yan kallon sun nuna rashin amincewarsu da daga tuta da kuma rera taken haramtacciyar kasar Isra'ilan da aka yi a dakin wasan, lamarin da ya sanya wasu daga cikinsu ficewa daga dakin taron don nuna rashin amincewarsu da hakan.
Kasar Aljeriya dai tana daga cikin kasashen da suke ci gaba da nuna goyon bayansu ga al'ummar kasar Palastinu da kuma kin kulla duk wata alaka ta diplomasiyya da HKI.