An Kai Hari Akan Tawagar Shugaban Majalisar Koli Ta Mulkin Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29121-an_kai_hari_akan_tawagar_shugaban_majalisar_koli_ta_mulkin_kasar_libya
Tashar talabijin din aljazera ta ambato ofishin Abdurrahamn Suwaihili yana cewa; An bude wuta akan ayarin motocinsa ne a yayin da yake ziyartar wasu garuruwa biyu da ke yammacin kasar
(last modified 2018-08-22T11:31:34+00:00 )
Mar 16, 2018 06:17 UTC
  • An Kai  Hari Akan Tawagar Shugaban Majalisar Koli Ta Mulkin Kasar Libya

Tashar talabijin din aljazera ta ambato ofishin Abdurrahamn Suwaihili yana cewa; An bude wuta akan ayarin motocinsa ne a yayin da yake ziyartar wasu garuruwa biyu da ke yammacin kasar

Sanarwar ta ci gaba da cewa; An jikkata mutane biyu da suke a cikin tawagar yayin da aka sace wasu 'yan sanda hudu.

Wannan shi ne karo na biyu da al-Suwaihili yake tsallake rijiya da baya sanadiyyar harin da ake kai masa.

A ranar 20 ga watan Febrairu na 2017 an kai wa Abdurrahman al-Suwaihili hari tare da pira ministansa Fayez al-suraj a birnin Tripoli.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da harin da aka kai wa Suwaihali tare da jaddada muhimmancin kauracewa amfani da karfi domin cimma manufofin siyasa.