Kasashen Tafkin Chadi Sun Sha Alwashin Gamawa Da Kungiyar Boko Haram
(last modified Fri, 16 Mar 2018 11:08:20 GMT )
Mar 16, 2018 11:08 UTC
  • Kasashen Tafkin Chadi Sun Sha Alwashin Gamawa Da Kungiyar Boko Haram

Kasashen tafkin Chadi tare da kasar Benin sun sanar da aniyarsu ta yin duk abin da za su iya wajen ganin bayan kungiyar kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya jiyo wasu kafafen watsa labaran kasar Chadi suna bayyana wannan labarin na aniyar da kasashen yankin Tafkin Chadin (wato Nijeriya, Nijar, Kamaru da Chad) bugu da kari kan kasar Benin na suka dauka na ganin bayan kungiyar Boko Haram din wacce ta ke ci gaba da ayyukan ta'addanci a yankin.

Rahotannin sun kara da cewa daga cikin matakan da wadannan kasashen suka dauka har da wani shiri na ba da horo na musamman ga wasu zababbun sojojin kasashen da aka kira shi da sunan Unifight Focus 2018 da nufin kaddamar da hare-hare kan 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Wannan shiri na horarwar dai yana daga cikin tsarin da sojojin hadin gwiwa na wadannan kasashe suka kaddamar da nufin ganin bayan ta'addanci a yankin musamman kungiyar Boko Haram.